YADDA ZAKA BAR GBWHATSAPP ZUWA NORMAL WHATSAPP BA TARE DA KA RASA KOMAI NAKA NA GB BA
LAMBA 1
Da farkon fari idan ka shirya barin GB zuwa kan normal to abinda zaka fara shine yin Backup akan GB ɗinka, Backup dai wanda aka saba, zakaje settings na GB ba kuma GB Settings ba, Aa settings normal na can ƙasan menu ɗin GB ɗinka, sai kace Account daga nan zakaga BackUp Chat, sai kayi kawai.
Abin Lura! Daga sanda kadanna Backup to zai fara naÉ—ar bayananka na can baya har zuwa kan sanda kace yayi backup É—in, bayan kagama backup duk wani chart da zakaÆ´i to baya cikin backup É—in dakaÆ´i, dan haka idan bakaso karasa komai to da zarar ka shirÆ´a backup kawai kaÆ´i kada kaÆ´i chart da kowa.
LAMBA 2
Idan kagama Back Up sai kaje kan Folders É—in wayarka wato File Manager zakaga Folder mesuna GBWhatsApp to kaÆ´i rename É—inta zuwa sunan whatsapp wanda kakeso zaka koma, misali akwai Whatsapp guda biÆ´u a play store kuma duk official ne wato na kamfanin whatsapp ne.
Akwai WhatsApp akwai kuma WhatsApp Business to wanda ka shirÆ´a kanaso ka koma kansa to sunansa zaka sauÆ´awa GBWhatsApp, ma'ana folder mesuna GBWhatsApp sai ka sauÆ´a mata suna zuwa WhatsApp Ko WhatsApp Business.
Daga nan sai kashiga cikin ita folder É—in daka sauÆ´awa suna, zakaga *Media* sai kashiga cikin Media duk wasu folders dake cikin Media suma zaka sauya musu suna zuwa sunan whatsapp É—in da zaka koma É—in.
A irin folders É—in dake cikin Media akwai irin su:
GBWhatsApp Images
GBWhatsApp Audio
GBWhatsApp Video
Da sauransu dai, to waÉ—annan duk sai ka sauÆ´a musu suna zuwa sunan wanda kake tunanin zaka koma kansa, misali ace kan WhatsApp Business zaka koma, to waÉ—annan can folders É—in duk zasu koma kamar haka ne:
WhatsApp Business Images
WhatsApp Business Audio
WhatsApp Business Audio
Haka dai duk zakabi duk wata folder dake cikin Media ka sauÆ´a mata sunanta.
Daga nan idan kagama sai ka tabbatar acikin *Databases* akwai wani abu wanda baƴa taɓuwa, shi wannan abin shine backup ɗinka, kada ka gogeshi. Databases zakaganta idan kashiga folder ta farko wadda ka sauƴamata suna daga GBWhatsApp zuwa sunan wanda kakeso kakoma, zakaga Data Base, to kaduba ciki idan kaga wani abu shikenan.
LAMBA 3
Kaga kagama Backup sannan kagama sauyawa faldoji suna, abinda yarage kawai kaje play store kaÉ—auko wanda kakeso, walau WhatsApp ko WhatsApp Business.
Idan ka saukeshi sai kasaka lambarka, zasuce maka ai lambarka tana kan wani whatsapp daban, kanaso a cireta daga É—aÆ´an, sai kace eh, kawai zai tafi loading daga nan zai lalubo backup É—inka, farko zai tambaÆ´eka cewa zai shiga wayarka yaga ko kanada Backup sai kace tom ta hanÆ´ar danna Continue daga nan zai cemaka yasamo backup É—inka, sai kadanna Next daga nan kuma zai ce maka yasamo backup na messages adadi kaza me girman size kaza, sai kataÉ“a  Restore daga nan sai kajira yagama Restoring É—in backup É—inka, shikenan idan yagama zai wuce sai ka Æ™arasa.
Zakaga komai naka yadawo daga kan snda kaÆ´i Backup zuwa can baya, Files ne kawai zakaga idan kaje viewing zkaga bazasu buÉ—uba, sbd ba takan sabon whatsapp É—in ka turasu ba, amma idan kaje can folder wadda ka sauÆ´awa suna zakaga komai naka na GB É—in.
(AIA ~ 2019 ®)